Burtaniya zata kayyade ma'aikata 'yan kasashen waje

Image caption Pira Ministan Burtaniya, David Cameron

Gwamnatin Burtaniya ta bada sanarwar kayyade adadin ma'aikata 'yan kasashen waje da zasu rika shiga Burtaniya domin neman aiki daga kasashen da ba na tarayyar turai ba.

An kayyade adadin zuwa dubu ashirin da daya da dari bakwai, sai dai hakan bai hada da dubban ma'aikatan da kampanoninsu ke masu sauyin wurin aiki zuwa Burtaniya ba.

Wannan dai na daga cikin manufofin gwamnatin hadin gwiwar Burtaniyar wadda ke son rage yawan bakin dake shiga kasar zuwa 'yan dubbanni.

An shafe shekaru kusan goma dai, ana samun mutane kusan dubu dari biyu na yin kaura zuwa Burtaniya a kowace shekara.