An bayyana Alhamis a matsayin ranar makoki a Cambodia

Kasar Cambodia
Image caption 'Yan kasar Cambodia zasu yi zaman makoki ranar alhamis dake tafe domin nuna alhininsu game da daruruwan mutanen da suke mutu.

Fira Ministan Cambodia ya ayyana ranar Alhamis dake tafe a matsayin ranar makokin mutuwar mutane kusan dari uku da hamsin sakamakon wata hatsaniya a lokacin wani buki a babban birnin kasar na Phnom Pehn.

Gwamnatin Cambodia tayi wannan sanarwa ne yayin da ake cigaba kokarin gano gawarwakin wadanda suka mutu a hatsaniyar da kuma ta jikkata wasu daruruwan mutanen

Shi dai wannan biki da ake kira na ruwa, shi ne mafi girma da ake yi kowacce shekara a birnin Phnom Pehn, kuma mazauna kauyuka kan yi tururuwa domin halartar bukin.

Wannan dai shine wani bala'i mafi muni daya taba faruwa a tarihin wannan biki da ake gudanarwa shekara-shekara