Koriya ta Arewa da ta Kudu na zargin juna

Ana zaman dar dar a yankin Koriya
Image caption Jiragen yakin Koriya ta Arewa ne suka kai hari a tsibirin Yeonpyeong

Kasashen Koriya ta Arewa da koriya ta Kudu na zargin juna da fara kai hare-hare, a wata hatsaniyar kan iyaka mafi muni da ta faru tun bayan karshen yakin Koriya.

A wata musayar wuta da aka kwashe kimanin sa'a guda ana yi, an harba makaman atilare daga Koriya ta Arewa zuwa wani tsibirin Koriya ta Kudu da ke kusa da kan iyaka.

Sojoji biyu ne dai a ka kashe, sannan a ka kuma raunata mutane kimanin hamsin da suka hada da sojoji da fararen hula.

Koriya ta Arewa ta ce Koriya ta kudu ce ta fara bude ma ta wuta, sai dai Koriya ta Kudun ta ce tana atisayi ne a kusa da tsibirin, amma ba ta harba makamai zuwa sashen Koriya ta Arewa ba.