Najeriya ba za ta yanke hulda da Iran ba

Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad

Gwamnatin Najeriya ta ce ba zata yanke huldar jakadancin dake tsakaninta da Iran ba, sakamakon takaddamar da ta kaure a tsakaninsu, saboda makaman da hukumomi suka kama a gabar tekun Lagos, wadanda aka ce sun fito ne daga kasar Iran.

Gwamnatin ta ce har yanzu tana ci gaba da gudanar da bincike akan batun.

Jam'ian tsaron SSS ne suka gano makaman,wadanda suka ce an biyo da su ta kasar ne domin kai su kasar Gambia.

Isra'ila ta yi zargin cewa, za a aike ne da makaman zuwa ga kungiyar Falasdinawa ta 'yan gwagwarmaya, watau Hamas, duk da yake kungiyar ta musanta zargin.

A jiya ne kasar Gambia ta bayyana yanke dukan huldar jakadancin da ke tsakaninta da Iran.