Aung San Suu Kyi ta yi ido hudu ta danta

Aung San Suu Kyi
Image caption A karon farko cikin shekaru goma Aung San Suu Kyi tayi ido hudu da danta mai suna Kim Aris

A Karon farko cikin shekaru goma jagorar fafutukar dimukradiyya a kasar Burma, Aung San Suu Kyi wadda aka sako daga daurin talala, ta yi ido hudu da danta.

Shi dai dan mai suna Kim Aris wanda ke zaune a Birtaniya ya hadu da mahaifiyar tasa ne a filin saukar jiragen sama na birnin Rangoon

Kim Aris dai ya shiga kasar ta Burma ne ta kasar Thailand inda ya jima a can kafin a bashi izinin shiga garin da mahaifiyar tasa take

A baya dai Kim Aris yasha yunkurin shiga garin na Rangoon ba tare da an bashi izini ba

Jami'an ofishin jakadancin kasar birtaniya sun bayyana ziyarar tasa zuwa Rangoon da cewar bata da nasaba da siyasa