An tsaurara matakan tsaro a Ivory Coast

Kasar Ivory Coast
Image caption An tsaurara matakan tsaro a kasar Ivory Coast a cigaba da shirye shiryen shiga zagaye na biyu na zaben shugabankasar

A cigaba da shirye-shiryen yin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Ivory Coast da za'ayi ranar Lahadi mai zuwa, an tsaurara matakan tsaro a duka fadin kasar.

Yanzu haka dai ana shirin baza karin soja dubu biyu a duk fadin kasar ta Ivory Coast.

Suma dai tsoffin 'yan tawaye na kungiyar New Forces dake iko da arewacin kasar suna kara baza dakarunsu na sa kai.

An dai samu rahotannin gwazba fada a birnin Abidjan, tsakanin magoya bayan 'yan takarar da zasu fafata a zagaye na biyu na zaben.