Najeriya ta daina tuhumar kamfanin Siemens

Kamfanin Siemens
Image caption Kamfanin Siemens

Babban kamfanin sadarwa na Siemens ya amince ya biya gwamnatin Najeriya Naira Biliyan 7 a matsayin tara, domin dakatar da karar da hukumar EFCC ta kai kamfanin, bisa zargin bada cin hanci ga wasu jami'an gwamnati a lokutan baya.

A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, babban mai sharia na kasar Mohammed Bello Adoke, ya ce gwamnatin kasar ta amince da wannan yarjajeniya ne, ganin yadda kamfanin na Siemens ya nuna nadama kan abinda ake zarginsa da aikatawa, da kuma daukar alkawarin sauya hali.

Wasu 'yan Najeriya na adawa da matakin sasantawa da kamfanin na Siemens, suna masu cewar kamata yayi a ci gaba da tuhumar sa a kotu.