Ana shirin fitar da sakamakon zaben Afghanistan

Zaben kasar Afghanistan
Image caption Yawancin 'yan takarar dake samun goyan bayan Shugaba Karzai basu taka rawar gani ba a zaben majalisar dokokin kasar

Nan gaba kadan a yau ne ake sa ran za'a fitar da sakamakon karshe na zaben 'yan majalisar dokokin Afghanistan mai cike da takaddama.

Wakilin BBC a birnin Kabul yace, yawancin 'yan takarar dake samun goyon bayan shugaba Hamid Karzai basu taka rawar gani ba a zaben.

Kuma an ce, shugaba Karzai ya damu da yadda batun kabilanci ya fito fili a zaben, inda 'yan takara da dama 'yan kabilar Pushto suka sha kaye a zaben.

Tuni dai aka ambato babban lawyan gwamnatin Afghanistan din yana cewa, yana tattara shaidun da zai yi amfani dasu wajen dakatar da wasu manyan jami'an hukumar zaben kasar.