Biranen Afirka za su cika makil nan da shekaru 40

Mutanen Afirka
Image caption Yawan mutanen dake rayuwa a manyan biranen kasashen Afirka zai ninka har sau uku nan da shekaru 40

Sabon rahoton hukumar muhalli ta majalisar dinkin duniya yace, yawan jama'ar dake zaune a manyan biranen kasashen Afirka zai ninka har sau uku nan da shekaru arba'in

Majalisar dinkin duniya ta kuma yi jan kunnen cewa, karuwar yawan al'ummar Afirka dake zaune a birane ka iya haddasa wani babban bala'i, idan har gwamnatoci basu dau matakan samar da muhalli da kuma sauran bukatun yau da kullum ba.

Hukumar ta muhalli ta majalisar dinkin duniya ta kuma ce, Afirka ce kan gaba a duniya wajen karuwar yawan jama'a a birane.