A yau ake gudanar da makoki a Cambodia

Makoki a kasar Cambodia
Image caption Shugaban Cambodia na jagorantar makokin mutanen da suka hallaka a ranar bikin ruwa a kasar

Kasar Cambodia ta soma makokin jimamin rashin daruruwan mutanen da suka mutu ranar litinin sakamakon wata hatsaniya a lokacin bukin ruwa na shekara-shekara a babban birnin kasar Phnom Penh.

An dai sauko da tutoci kasa, kuma gwamnati ta bada umarnin rufe dukkan wuraren shakatawa dake kasar a duk tsawon yau

Wakilin BBC yace rahotonnin farko dai sun ce, motsin da gadar dake kusa da wurin bukin ta yi ne ya haddasa hatsaniyar da ta hallaka jama'a.

FiraMinistan Cambodia Hun Sen da matarsa ne ke jagorantar makokin a kusa da gadar da lamarin ya auku.

Manyan jami'an gwamnatin kasar cambodian sunyi layi domin girmamawa ta karshe ga mutanen da suka mutu

Alkaluman baya bayan nan dai na nuni da cewar mutane dari uku da hamsin ne suka mutu