Masu hakar ma'adinai 29 sun mutu a New Zealand

Iyalan masu hakar ma'adinan da suka mutu a New Zealand
Image caption Mahakan ma'adinan kasar New Zealand ashirin da tara da suka makale a karkashin kasa sun mutu

Masu hakar ma'adinai ashirin da tara da suka makale a karkashin kasa kwanaki biyar da suka gabata a New Zealand sun mutu.

'Yan sanda kuma sun ce, anji wata kara mai tada hankali a mahakar ma'adinai dake Greymouth a yau din nan.

Wannan kuma yasa an daina fatan samun wani daga cikin masu hakar ma'adinan da rai.

Fira Ministan New Zealand John Key, wanda tun farko ya ja kunne dangane da bala'in da ka iya aukuwa, yace, yanzu haka kasar tana cikin makoki.

Ya kuma kara da cewa, za'a yi cikakken bincike dangane da yadda lamarin ya auku da nufin ganin hakan ba ta sake aukuwa ba.