Sojojin ruwan Nigeria sun kama makamai a Lagos

makamanda aka kama a kwanakin baya
Image caption makamanda aka kama a kwanakin baya

Rundunar sojojin ruwa ta Nijeriya ta kama wasu motoci, wadanda ke dauke da makamai a cikinsu.

Rundunar sojin ruwan ta ce ta kama mutane biyu bisa zarginsu da hannu wurin safarar wadannan makamai.

An kama makaman ne a birnin Lagos dake kudu maso yammacin kasar inda nan ne daya daga cikin hanyar shige da fice da kayayyaki daga kasashen ketare.

Wannan shi ne karo na ukku da hukunmomin tsaro na Nijeriya suke kama makamai a birnin na Lagos.

Jama'a dai na nuna fargaba game da kama irin wadannan makamai yayin da zabuka suke karatowa a kasar.