Amurka da Koriya ta Kudu za su yi atisaye

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Amurka na shirin baiwa Koriya ta Kudu kariya daga dukkan wani hari da Koriya ta Arewa zata iya kai mata

Amurka da Koriya ta kudu za su yi atisayen soja na hadin gwiwa nan gaba kadan a wani martani ga harin makamai masu linzami da Koriya ta Arewan ta kai a kan wani tsuburi na Koriya ta kudu a ranar Talata.

An gano gawarwakin wasu ma'aikatan kamfanin gine-gine biyu, wadanda suka mutu sakamakon harin na Koriya ta Arewa.

Har ila yau sojoji sun rasa rayukansu sanadiyyar wannan hari.

Shugaba Obama dai ya ce Koriya ta Arewa ta zama wata barazana da dole ne a yi maganinta.

Shugaba Obama ya kuma ce, Koriya ta kudu wata babbar kawa ce da Amurka za ta baiwa kariya daga duk wata barazana.