Alamura sun tsaya cik a kasar Portugal

yajin aiki a kasar Portugal
Image caption yajin aiki a kasar Portugal

Al'amura sun tsaya cik a kasar Portugal sakamakon wani yajin aiki da ma'aikata suke yi game da matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin kasar take dauka.

Harkokin sufuri da na lafiya, da kwashe shara da na jiragen-sama duk sun gamu da cikas.

Wannan shi ne babban yajin aikin da aka gudanar a kasar a sama da shekaru ashirin.

Gwamnatin kasar mai ra'ayin gurguzu ta hakikance cewa rage kudade da gwamnati take kashewa, da kuma kara haraji suna da matukar muhimmanci wajen kaucewa kasar Portugaal ta zama ita ce kasa ta ukku bayan Girka da Ireland da zasu bukaci tallafi daga kasashen dake amfani da kudin Euro.