Kungiyar Boko Haram ta ce za ta kai karin hare-hare

Tsohon shugaban Boko Haram, marigayi Muhammad Yusuf
Image caption Tsohon shugaban Boko Haram,marigayi Muhammad Yusuf

Kungiyar Boko Haram ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare a kan jamian tsaron Najeriya, a ci gaba da rikicin da suke yi da gwamnatin kasar.

Kungiyar ta ce za ta yi hakan ne sakamakon sanyin jikin da jami'an tsaro na farin kaya suka yi a tattaunawa da su domin kawo sulhu.

Wani mai magana da yawun kungiyar wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, sun fara tattaunawar zaman lafiya da jami'an tsaron na Najeriya sama da wata daya da ya gabata.

Sai dai ya ce daga bisani jami'an tsaro suka saba yarjejniyar inda suka ci gaba da kama 'ya'yan kungiyar.