Yan sandan Brazil sun kudiri anniyar murkushe tarzoma

Taswirar Brazil
Image caption Taswirar Brazil

'Yan sanda a birnin Rio de janeiro na Brazil sun tura tankokin yaki zuwa wata unguwar talakawa domin kwantar da wata tarzoma da ta hallaka akalla mutane ashirin da takwas a kwanakin nan.

Ministan tsaron kasa, Jose Mariano Beltrame ya ce tankoki shida aka tura shake da yan sanda da ke dauke da makamai zuwa Vila Cruzeiro da ke arewacin birnin.

Kwanaki biyar da suka wuce ne dai rikici ya barke a unguwar tsakanin jami'an tsaro da dillalan miyagun kwayoyi.

Wani kyaftin din yan sanda da ke cikin masu kwantar da tarzomar ya ce a shirye suke su ga cewa sun murkushe masu tarzomar.