Ana shirin kafa sabuwar gwamnati a Iraki

An zabi Praministan Iraki, Nouri al Maliki don ya kafa wata sabuwar gwamnati, abun da ya kawo karshen rashin tabbas din da aka shafe watanni takwas ana fuskanta, tun bayan babban zaben da aka yi a kasar, inda babu jam'iyyar da ta samu nasara gaba-gadi.

Yanzu dai Mr Malikin yana da kwanaki talatin don gudanar da tattaunawa da abokan kawancensa dangane da irin mukaman da za su rarraba a tsakaninsu.

Ana sa ran sabuwar gwamnatin za ta hada da dukkan manyan bangarorin kasar, watau 'Yan Shi'a da 'yan Sunni da kuma Kurdawa.

Wannan shi zai baiwa Nouri al-Maliki damar yin wa'adi na biyu na mulki a Irakin.