Tuhuma dangane da yunkurin shigo da makamai cikin Nijeriya

Wasu daga cikin makaman da aka kama a Lagos
Image caption Ana zargin cewa makaman sun fito ne daga Iran

Wata kotu a Najeriya ta tuhumi mutane hudu dangane da makaman da aka kama a watan jiya a gabar ruwan Lagos.

Uku daga cikinsu wadanda duk 'yan Najeriya ne sun musanta tuhumar da ake yi musu ta safarar makamai.

Na hudunsu kuma wanda jami'in kasar Iran ne ya ce ya na bukatar wakilci daga ofishin jakadancin kasarsa kafin ya bada bayani game da tuhumar da ake yi masa.

Makaman dai sun hada da bindigogin harba roka, da gurneti, da bama-bamai da aka same su cikin wasu manyan akwatuna da aka dauko daga kudancin Iran da nufin kaiwa kasar Gambia.