Matakan fadakarwa kan ciwon suga a Borno

Hukumomin lafiya a jihar Borno ta Nijeriya sun shirya wani gangamin fadakar da jama'a game da illar ciwon suga, wato Diabetes.

Bayanai daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta fitar sun nuna cewar ciwon suga na ci gaba da hallaka jama'a a kasashe da dama.

An kiyasta cewar sama da mutane miliyan dari biyu da shirin ne a duniya ke dauke da ciwon suga.

A jihar Bornon kungiyar masu Fama da Ciwon Suga tare da likitoci, da ma'aikatan jinya a jihar Borno sun halarci wannan gangamin fadakarwa ne tare da yin gwaji da tantance masu dauke da cutar domin kokarin rage karuwar matsalar a tsakanin al'umma.