Koriya ta Kudu ta nada sabon ministan tsaro

Sojin ruwan yakin Koriya ta Kudu
Image caption Gwamnatin Koriya ta kudu ta nada sabon ministan tsaro kwana guda bayan mai rike da mukamin yayi murabus

Gwamnatin Koriya ta kudu ta nada sabon ministan tsaro, kwana guda bayan mai rike da mukamin, Kim Tae-Young yayi murabus

Kim Tae Young dai yayi murabus ne sakamakon sukar da aka yi masa na yin nawa wajen maida martani ga hari da makamai masu linzami da Korita ta Arewa ta kai cikin makon nan

Shi dai sabon ministan tsaron na Koriya ta kudu, tsohon cikakken janar din soja ne

Yana kuma da ra'ayin kasancewar sojan Koriya ta kudu masu azama wajen gano take-taken Korea ta arewa, da kuma maida martani ga duk wani harin da ta kai nan take.