Yiwuwar barkewar yaki a yankin Koriya

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-il
Image caption Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-il

Koriya ta Arewa ta ce atisayen hadin gwiwa da aka shirya gudanarwa tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka a karshen makon nan, ya na kara kusantar da yankin ga tsunduma cikin yaki.

Kwanaki uku bayan musayar wuta mafi muni a cikin shekaru masu yawa tsakanin kasashen Koriyar ta Arewa da ta Kudu, an sake jin amon bindogogin atilare daga Koriya ta Arewa, amma babu wani makami da ya fada yankin Koriya ta kudu.

Babu bayyani a kan wurin da Korea ta Kudun da Amurka zasu yi atisayen nasu ba, amma China ta yi gargadin cewa, ba zata yarda da duk wani atisayen soja a yankin ruwan da yake karkashinta ba.