Rauf Aregbesola ne zababben gwamnan Osun

Image caption Rauf Aregbesola

A Najeriya Kotun daukaka kara ta tarayya da ke Badun (Ibadan), ta yanke hukuncin cewa Rauf Aregbesola na jam'iyyar AC ne ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun wanda aka gudanar a watan Afrilun shekarar 2007.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne dai bayan an kwashe shekaru uku ana ta shari'a.

Shi dai dan takarar jam'iyyar ta AC ya daukaka kara ne yana neman kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe wadda ta tabbatar da cewa dan takarar jam'iyyra PDP, Olagunsoye Oyinlola ne ya lashe zaben.

Bayan kotun daukaka karar ta amince da bukatun Aregbesola, ta kuma ba da umurnin a rantsar da shi gobe.

Wannan hukunci ya zo ne makwanni kadan bayanda wata kotun daukaka kara da ke Ilori, ta tabbatar da dan takarar jam'iyyar AC Fayode Kayomi, a matsayin zababben gwamnan jihar Ekiti.

Hukuncin Sokoto

A yanzu dai jam'iyyar ta AC na da kujerun gwamnoni uku a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Abin da masu lura da al'amura ke ganin zai iya taimakawa jam'iyyar a zabukan da za a gudanar masu zuwa.

Har ila yau a Najeriyar, kotun kolin kasar da ke Abuja ta yi watsi da shari'ar da ke gaban kotun daukaka kara ta jihar Sokoto, wadda Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi na jam'iyar DPP ya shigar gabanta.

Dan takarar na DPP yana kalubalantar zaben Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin gwamnan jihar.

Wannan hukunci da kotun kolin ta zartar dai ya kawo karshen takaddamar da ake ta yi dangane da zaben gwamna Jihar.