Shakar hayakin taba na kashe mutane 600,000

Hayakin taba sigari
Image caption Bincike ya gano cewar shakar hayakin tabar da wasu kesha na kashe mutane akalla dubu dari shida a kowacce shekara

Nazari na farko a duniya dangane da illar da shakar hayakin tabar da wasu ke busawa ga jama'a ya gano cewa, lamarin kan haddasa mutuwar mutane akalla dubu dari shida, yawancinsu yara kanana, a kowacce shekara.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato WHO ce dai ta gudanar da wannan bincike a kasashe kusan dari biyu

Shakar hayakin taba sigari da wasu ke busawa na haddasa kamuwa da cututtukan da kan kama masu shan taba sigarin, da suka hada ciwon zuciya, da kuma cututtukan da suka shafi numfashi.

Mawallafan binciken sun nuna matukar damuwarsu kan yadda hayakin tabar ke yin illa ga kananan yara, lamarin dake janyo masu cututtuka irinsu numomiya da kuma asma