Kotun kolin Najeriya tayi watsi da kara akan gwamnan Sakkwato

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, Kotun kolin kasar dake Abuja, ta yi watsi da shari'ar dake gaban kotun daukaka kara ta jihar Sakkwato, wadda Alhaji Muhammadu Maigari Dyingyadi na jam'iyar DPP ya shigar, yana kalubalantar zaben Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin gwamnan jihar.

Wannan hukunci da kotun kolin ta zartar a yau, ya kawo karshen takaddamar da ake ta yi dangane da zaben gwamna Jihar.

An dauki tsauraran matakan tsaro a birnin Sakkwato, domin gudun barkewar tashin hankali bayan hukuncin na yau.