An kame mutane goma sha biyu a Iraki

Taswirar kasar Iraki
Image caption Taswirar kasar Iraki

Hukumomi a kasar Iraki sun ce sun kame mutane goma sha biyu wadanda ake zargi da hannu a harin da aka kai a wata majami’a a birnin Bagadaza a watan da ya gabata.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce wadansu daga cikin masu tayar da kayar bayan da suka fi hadari a Bagadaza na cikin mutunen da aka kama, ciki har da shugaban wata kungiyar da ke da alaka da Al-Qaida wacce ta ce ita ta kai harin.

Hukumomin sun kuma ce sun kwace kayayyakin hada bama-bamai kuma wadanda ake zargin sun dauki alhakin kai wadansu hare-hare.

Fiye da mutane hamsin ne dai aka kashe a harin kafin jami'an tsaro su fada majami’ar su kubutar da wadansu mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.