Ana jana'izar sojojin Koriya Ta kudu

Sojojin Korea ta kudu
Image caption Ana jana'izar sojojin Korea ta kudu

Gidajen talabijin na Koriya ta kudu na nuna jana'izar da ake yiwa sojoji biyun da makaman atilaren Koriya ta arewa suka kashe a ranar Talata.

Kwamandan sojin kasar, Manjo Janar You Nak-Joon ya shaidawa masu makoki a wani asibitin soji da ke daura da Seoul babban birinin kasar cewa, za su dauki fansar kisan dakarun nasa.

Ya ce:''Gaba daya dakarun Koriya ta kudu za mu rike wannan fushi da gaba har cikin bargonmu, kuma zamu tabbatar mun dauki fansa kan Koriya ta arewa''.

Jana'izar na zuwa ne a daidai lokacin da Koriya ta Kudu da Amurka ke shirin gudanar da atisayen sojan ruwa, China kuma ke kokarin sasanta rikicin.