Rundunar 'yan sanda ta sassauta dokar hana zirga-zirga a Maiduguri

'Yan sanda Nijeriya
Image caption 'Yan sanda Nijeriya

Rundunar 'Yan sandan jihar Borno ta bayar da sanarwar sassauta dokar hana zirga-zirgar motocin haya a birnin Maiduguri.

Ta ce yanzu zata fara aiki ne daga misalin karfe shida na safe zuwa takwas na dare sabanin shida na yamma.

Wannan kuwa ya biyo bayan irin koke-koken da jama'a da dama ke yi ne cewar dokar na takura wa harkokinsu na yau da kullum.

Haka nan kuma akwai bayanai da suka nuna cewar kungiyar direbobin jihar na shirin yin wata zanga-zanga a gobe game da wannan doka.

Rundunar 'Yan sandan jihar Bornon ta dauki wannan mataki ne kwana biyu bayan da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka yi amfani da karamar mota wajen kai hari tare da bindige wasu 'yansanda biyu har lahira, sabanin baburan da su kan yi amfani da su.