Ana cikin fargaba a kasashen Korea

Mazauna garin Yeonpyeong wanda Korea ta arewa ta akiwa hari
Image caption Ana zaman zulumi a yankin Korea

A lokacin da Amurka da Koriya ta kudu suka fara atisayen kwanaki hudu na sojin ruwa, an umarci mazauna tsibirin kan iyakar da Koriya ta arewa ta kaiwa hari a makon jiya da su buya a mafakar karkashin kasa.

An bada umarnin ne bayan da rahotanni suka ce an ji karar hare-haren rokoki a tsibirin na Yeonpyeong amma daga bisani an janye umarnin.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta kudu ya ce Koriya ta arewa na matso da makamai masu linzami daura da kan iyakarta.

Koriya ta arewar ta yi gargadin kai hare-hare matukar atisayen da dakarun Amurka da na Koriya ta kudu ke yi ya keta iyakarta.

Sai dai a kokarinta na ganin ta hana gwabza yaki tsakanin kasashen na Koriya ta Kudu da ta Arewa, kasar China ta gana da shugaban Koriya ta Kudu, Lee Myung-Bak.