Kalubale ga sana'ar wasan kwaikwayo

Tutar Najeriya
Image caption Kalubalen da sana'ar fim ke fuskanta

A bana ne masana'antar shirya fina-finan Hausa wacce a ke yiwa lakabi da Kanywood, dake da tushe a birnin Kanon Najeriya, ta cika shekaru ashirin da kafuwa.

A kan haka ne, wani kamfanin shirya fina-finan Hausa da ke birnin na Kano mai suna Iyan Tama Multimedia, ya shirya wani taro a makon nan don murnar cika shekarun ashirin.

Taron ya duba irin kalubalen da sana'ar ta fuskanta cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Alhaji Abdulkarim Muhammad shi ne mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masu fina-finai ta Najeriya, ya shaidawa BBC cewa, sana'ar na fuskantar kalubale da dama.

Ya ce:''Kalubale na farko da har yanzu muke fama da shi, shi ne ilimi;harkar fim tana bukatarsa, saboda ana amfani da kayan ayyuka wadanda suke canzawa da lokaci.Sai kuma na samun kudi, inda mutane zasu so su zuba jari a fannin''.

Mahalarta taron sun koka kan yadda Hausawa ke amfani da al'adu da dabi'un wasu jama'a wajen shirya fina-finan.