Baiwa Ireland bashi: Ministocin Tarayyar Turai na taro

Ministocin kudi na tarayyar turai na wani taro da aka shirya na gaggawa a Brussels domin kokarin amincewa da sharudan bada bashin makudan kudaden da za a baiwa jamhuriyar Ireland.

Kasar at Ireland ta ce dukan bangarorin kowa na bukatar wata yarjejeniya game da kudaden tallafin, kafin a bude kasuwanin hada hadar kudi a gobe Litinin.

Daya daga cikin muhimman batutuwa shi ne na kudin ruwan da za a canza, inda wasu rahotani ke cewa mai yuwa ya yi yawan da zai zarta kima, ta yadda kasar ta Ireland zata gaza biyan bashin.

Bashin dai ana sa ran zai kai na dala biliyan dari da goma.

A jiya dubban mutane sun yi zanga-zanga a birnin Dublin suna nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin kasar ta Ireland.