Ana zabe zagaye na biyu a Ivory Coast

Zabe a Ivory Coast
Image caption Zabe a Ivory Coast

Masu kada kuri'a sun ja dogayen layuka a rumfunan zabe a kasar Ivory Coast, domin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Shugaba mai ci yanzu, Laurent Gbagbo ne ke takara da tsohon Firaministan kasar kasar, Alasane Ouattara, a wani abin da ake yi wa kallon , za a yi kare jini biri jini.

Yakin neman zaben dai ya kasance da tashin hankali, inda ta kai an sa dokar hana fitar dare.

Mutane akalla uku ne aka kashe a birnin Abidjan a jiya, lokacin wata zangar-zangar adawa da dokar hana fitar.