Mutane takwas sun mutu a Pakistan

Masu aikin ceto a lokacin wani hadarin jirgi a Pakistan
Image caption Mutane takwas sun mutu a hadarin jirgin Pakistan

Akalla mutane takwas ne suka rasu a Pakistan bayan da wani jirgin saman daukar kaya ya fadi jim kadan bayan tashi daga filin jiragen sama na Karachi.

Gaba daya wadanda suka rasun 'yan kasar Rasha ne da ke tuka jirgin saman kirar Rasha zuwa Sudan.

Wannan shi ne karo na uku da jirgin sama ya fadi daura da filin jiragen na Karachi a watannin baya-bayan nan.

A watan Yuli hatsarin ya hallaka mutane dari da hamsin, mako uku da suka wuce kuma mutane ashirin da uku ne suka rasu yayin wani hatsarin jirgin saman.