Kwarmato: Jaridun duniya sun fara buga muhimman sirrin Amruka

Yanzu haka dai wasu jaridu na kasashen duniya sun fara wallafa wasu abubuwa da ake ganin muhimman bayanan sirri na Amurka, bayan da shafin intanet din nan na Wikileaks mai kwarmata bayanan sirrin da aka tsegunta masa, ya yi biris da rokon da gwamnatin Amurka ta yi masa na kada ya yi hakan.

Ya zuwa yanzu an buga bayanai kimanin dubu dari biyu da hamsin.

Wakilin BBC ya ce Wikileaks ya buga wasu bayanai na irin rokon da kasashen Larabawa ke yi wa Amurka cewa ta dauki dukkan matakan da zata iya wajen hana shirin nukiliyar kasar Iran, ciki har da karfin soja.

Haka nan kuma akwai bayanan dake nuna cewa Amurkar na leken asirin dukkan abubuwan da shugabannin Majalisar Dinkin Duniya ke yi, ciki har da Sakatare Janar Ban Ki-moon.