Yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Taswirar Najeriya
Image caption Hukumomi na taro kan cutar malaria a Bauchi

Hukumomin lafiya a jihar Bauchin Nijeriya na hada gwiwa da 'yan jarida wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro data gallabi jihar.

Hukumomin da 'yan jaridar na gudanar da tarukan karawa juna sani a fadin jihar da zummar wayarwa da jama'a kai kan muhimmancin tsabta da alkinta muhalli.

Hukumomin dai sun ce daukar wannan mataki ya zamo wajibi sabo da muhimmancin kafofin watsa labarai wajen fadakarwa da ilmantarwa.

Sai dai 'yan jaridar na ganin hanya mafi dacewa ta yaki da cutar ta cizon sauro ita ce hukumomi su himmatu wajen tabbatar da muhalli mai tsafta da rage talauci, da kuma samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiyar jama'a.