Shugaban Korea ta kudu ya yi jawabi ga 'yan kasar

Shugaban Korea ta Kudu, Lee Myung-Bak
Image caption Koriya ta arewa za ta dandana kudarta

Shugaban Koriya ta kudu, Lee Myung-Bak, ya yi jawabi ga 'yan kasar a karo na farko tun bayan hare-haren da Koriya ta arewa ta kai kasar a ranar talatar da ta wuce, wanda ya hallaka mutane hudu.

A jawabin da ya yi a gidan talabijin na kasar, shugaba Lee ya ce, alhakin gaza kare wadanda abin ya shafa na wuyansa.

Ya ce Koriya ta arewa za ta dandana kudarta idan ta kara kai wani harin.

Shugaba Lee ya kara da cewa:''Sai mun samu karfin halin da ba ya ja da baya idan ya fuskanci hatsari ne da takala, sannan za'a samu tabbataccen zaman lafiya''.