Direbobin tankar mai na yajin aiki a Najeriya

Rijiyar mai a Najeriya
Image caption Rijiyar mai a Najeriya

A Nigeria, kungiyar direbobin tankar mai ta fara wani yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.

Kungiyar ta umurci dukan mambobinta da su dakatar da jigilar man fetur a duk fadin kasar, tun daga karfe 12 na daren jiya.

Kungiyar tana zargin jami'an tsaron kasar, musamman ma sojoji, da hallaka 'ya'yanta ba gaira ba dalili, da kuma kwace masu motoci.

A ranar 6 ga wannan watan Nuwamba ne aka kashe wani direban tankar mai, Malam Sa'idu Mohammad, a jahar Plateau.

Idan har yajin aikin ya dore, to kwa za a kara fuskantar matsalar karancin mai a gidajen sayar da man.