Matsanancin Halin Rayuwa: Tsawon rayuwar jama'a

Kashi na uku na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa ya duba tsawon rayuwar jama'a a duniya. Shekarun da jama'a ke shafewa kafin su mutu ya sha banban daga sassa zuwa sassa na duiniya - ko ta yaya ya shafi yadda jama'a ke rayuwa?

Adadin shekarun da jama'a ke fatan kaiwa kafin su mutu ya sha ban-ban - daga shekaru 83 a Japan zuwa 42, a Afghanistan da Zimbabwe.

A kasashe da dama da suka ci gaba, adadin shekarun da jama'a ke shafewa kafin su mutu ya karu a karni na 20, saboda ci gaba ta fuskar yanayin rayuwa da kuma nasarar da aka samu wajen kawar da mafi yawan cututtuka masu yaduwa.

A wasu daga cikin kasashe masu tasowa, karuwar ci gaba wajen rayuwar yara kanana da ci gaba ta fuskar kiwon lafiya ya kara adadin shekarun da jama'a ke rayuwa. Sai dai wasu kasashen na yankin Kudu da Sahara a Afrika sun fuskanci illa sosai daga cutar HIV/AIDS.

Kasar Japan ta fi kowacce kasa yawan tsofaffi. Fiye da kashi 20 cikin dari sun haura shekaru 65, kuma akwai kimanin mutane 44,449 da suka cika shekaru dari a watan Satumban bana, wato 2010.