Matsanancin Halin Rayuwa: Mahimmancin addini

Kashi na karshe na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa zai duba mahimmancin addini a rayuwar jama'a.

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa kashi 84 cikin dari na wadanda suka balaga, suna daukar addini a matsayin muhimmin bangare na rayuwarsu ta yau da kullum - babu sauyi a shekaru hudun da suka wuce.

Binciken wanda aka gudanar a kasashe 114 a bara, ya nuna cewa a kasashe goma da suka hada da Bangladesh da jamhuriyar Niger da Yemen da Indonesia, akalla kashi 98 cikin dari sun bayyana cewa addini na da muhimmanci a rayuwarsu ta yau da kullum.

Kasashen da ba su damu da addini sosai ba, su ne Estonia wacce ke da kashi 16 cikin dari, sai Sweden kashi 17 da kuma Denmark mai kashi 19 cikin dari.

Mabiya addinin Kirista da suka hada da Catholic and Protestant na ganin su ne suka fi yawa inda suke da mabiya biliyan biyu, yayin da addinin musulunci ke da mabiya biliyan daya da miliyan dari shida.