Matsanancin Halin Rayuwa: Matsalar tattalin arziki

A daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin farfadowa daga matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta, kashi na shida na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa zai duba saukin tafiyar da al'amuran kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.

Kasar Singapore ce ta zo ta daya a jerin da Babban Bankin duniya ya fitar na kasashen dake da saukin yin kasuwanci, inda Hong Kong ta zo ta biyu sai New Zealand ta uku. Kasar Chadi ce ta zo ta karshe a jerin kasashen 183.

Kididdigar ta duba yadda sauran al'amura ke da sauki kamar fara sabuwar wata harka ta kasuwanci.

A mafi yawan lokuta kasashen da suka ci gaba ne suke kokari sosai, yayinda kasashe masu tasowa da talakawa ke kasancewa kurar baya.