Matsanancin Halin Rayuwa: Ilimi

Kashi na biyar zai maida hankali ne kan ilimi. Adadin masu ilimi ya sha banban a duniya; a kasar Mali, kashi 26 cikin dari ne na wadanda suka haura shekaru 15 su ke iya karatu da rubutu. Yayinda a kasashe masu tasowa adadin ya kai kashi 99 cikin 100.

Yawancin kasashen dake da karancin masu ilimi suna Afrika, duk da cewa kasashen Bangladesh da Pakistan su ma suna da adadi mafi karanci na kashi 53 da 54 cikin dari.

A mafi yawan wadannan kasashe, maza sun fi samun damar yin karatu fiye da mata. Wata kididdiga ta kungiyar Plan International ta nuna cewa kashi uku cikin dari ne kawai na mata ke halartar makaranta a kasashen Mozambique da jamhuriyar Niger.

Kasar China ce ke da adadi mafi yawa na manyan makarantu a duniya - inda suke samar da ilimi ga kashi 25 cikin dari na manyan daliban duniya