Matsanancin Halin Rayuwa: Cin hanci

Zagaye na biyu na shirin Matsanancin Yanayin Rayuwa zai tattauna kan cin hanci. Wakilan BBC za su yi bincike kan kasashen Sweden da Somaliya - inda za su duba ko kasashen biyu na tafiya kamar yadda suke a zahiri.

An kara bayyana Somaliya a matsayin kasar da ta fi kowacce cin hanci a duniya - sama da kasashen da ke fama da yaki irinsu Burma da Afghanistan da Iraqi.

Kididdigar kungiyar Transparency International ta nuna cewa kasashen Denmark da New Zealand da Singapore a matsayin wadanda suka fi karancin cin hanci a duniya. Daga cikin kasashen da suka fuskanci koma baya a shekarun 2009 da 2010 sun hada da Italiya da Amurka. Yayin da Chile da Haiti suka samu ci gaba.