Binciken Google akan zargin karya ka'idar gogayyar cinikayya

Kamfanin Google
Image caption Kamfanin Google

Hukumar tarayyar Turai ta kaddamar da bincike a kan katafaren kamfanin nan na matambayi baya bata, watau Google, bayan zarge zargen da ake masa na yin amfani da babakeren da yayi a fannin, wajen karya ka'idojin gogayyar kasuwanci.

Kananan kamfanonin matambayi baya bata da dama sun zargi Google da cewa, yana tsara shafinsa ta yadda za a tura su can kasa a shafin yanar gizo.

Hukumar turan zata duba ko da gaske ne kamfanin na Google na tilastawa abokan huldarsa, daina sa tallace tallace a shafukan sauran kamfanonin da yake gogayya da su.

Kamfanin Google ya musanta zarge zargen. Amma ya ce zai bada hadin kai ga masu binciken.