Kwamitin IOC zai binciki Issa Hayatou

issa hayatu
Image caption Duka wadannan mutanen na cikin wadanda a ka zarga

Kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya ya ce zai binciki zargin cin hancin da BBC ta yiwa mataimakin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta FIFA Isa Hayatou, wanda mamba ne a kwamitin.

Kwamitin ya nemi BBC ta gabatar da shaidu kan zargin da ta yiwa manyan jami'an FIFA uku bayanda ya kalli shirin Panorama da gidan talabijin na BBC ya watsa. Shirin Panorama ya zargi Mista Hayatou da wasu jami'an FIFA biyu da ke da kuri'a a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya da karbar cin hanci a shekarun 1990.

Hukumar kwallon kafa ta FIFA dai ta yi watsi da zargin.

Kwamitin na IOC ya ce zai mika batun ga sashinsa na da'a.

Jami'an FIFA ba su da laifi

"Kwamitin IOC ya lura da zargin da shirin Panorama ya yi, kuma ya nemi wadanda suka shirya shirin su gabatar masa da shaidu. Kwamitin ba ya goyon bayan cin hanci ko kadan, don haka zai mika batun ga kwamitin sa na da'a," kamar yadda ya ce.

A ranar Talata, FIFA ta fitar da sanarwa tana cewa abubuwan da a ka yi zargin a kansu sun faru ne kafin shekara ta 2000, kuma tuni hukumomi a kasar Switzerland suka gudanar da bincike.

"A hukuncin da ta yanke a ranar 26 ga watan Yunin 2008, koton hukunta laifuka ta Zug ba ta samu wani jami'in FIFA da laifi ba."

Shirin BBC na Panorama, wanda aka watsa a ranar Litinin, ya zargi jami'an FIFA Issa Hayatou da Nicolas Leoz da Ricardo Teixeira, da karbar cin hanci daga wani kamfanin tallata hajar wasanni wanda a ka baiwa kwangila mai tsoka a gasar cin kofin duniya.

Duka mutanen uku dai za su kada kuri'a a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da 2022.

Ba su kuma maida martani da zargin da shirin na Panorama ya yi musu ba.

Ingila na gwagwarmaya da kasashen Rasha da Spain/Portugal da Netherlands/Belgium a kokarin daukar nauyin gasar ta 2018.