Kotu ta ki soke dokar shari'ar musulunci a Amurka

Shugaban Amurka, Barack Obama
Image caption Kotu ta ki soke dokar musulinci a Amurka

Wata kotun tarayya a Amurka ta dakatar da bukatar da masu zabe a jihar Oklahoma suka yi ta soke shari'ar Islama daga cikin tsarin shari'ar da aka amince da su a kasar.

Mai sharia Vicky Miles-Lagrange, ta umarci jihar Oklahoma kar ta fara aiki da wata doka, da za ta haramtawa alkalai mutunta tanade-tanaden shari'ar musulunci.

Ta ce ta na bukatar lokaci domin jinjina korafin wani musulmi da ya ce rashin aiki da shari'ar zai take masa hakkinsa na gudanar da addininsa, kamar yadda tsarin mulkin Amurka ya tanada.

A wannan watan ne dai al'umar jihar Oklahoma suka kada kuri'ar haramta aiki da shari'ar musulunci a zaben jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar yayin zaben 'yan majalisar dokoki.