Takaddama kan kudin da ake baiwa 'yan majalisa

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption Ana cece-kuce kan kudin da ake naiwa 'yan majalisa

A Najeriya, a yanzu haka wata takaddama ce ta kaure dangane da yawan kudin da ake baiwa 'yan majalisar tarayya daga kason da gwamnatin tarayya ke karba na kasafin kudin kasar.

Rikicin dai ya taso ne bayan da aka ambato shugaban babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi na cewa, ana baiwa 'yan majalisar kashi ashirin da biyar ne cikin dari daga cikin kasafin kudin, bayan kuwa ba sa aiwatar da wasu muhimman ayyuka.

Su ma masu sharhi kan tattalin arziki, sun ce baiwa 'yan majalisa wadannnan makudan kudade bai dace ba, idan aka yi la'akari da cewa mafi yawa daga cikin 'yan kasar na rayuwa ne cikin matsi.

Sai dai a nasu bangaren, 'yan majalisar sun ce bai kamata shugaban babban bankin ya yi wannan kalami ba, ba tare da la'akari da abin da gwamnati ke kashe masa ba.

Honourable Musa Sarkin Adar, dan majalisa ne, ya shaidawa BBC cewa: ''Da (shugaban babban bankin ya yi magani a kan 'yan majalisa, shi ya fadi nawa ya ke kashewa wajen gudanar da aikin sa?Ya fadi nawa ya ke dauka wajen tafiye-tafiyensa...bai kamata mutane su yi amfani da damar da suke da ita ba wajen fadawa mutane abin da ba daidai ne ba''.