Direbobin tankar mai sun janye yajin aiki a Najeriya

Rijiyar mai a Najeriya
Image caption Rijiyar mai a Najeriya

Kungiyar direbobin Tanka ta Nigeria, ta dakatar da yajin aikin da ta shiga jiya na gargadi, na tsawon kwanaki bakwai.

Hakan dai ya biyo bayan wata tattaunawa ce da shugabannin kungiyar suka yi da gwamnati a yau.

Kungiyar ta shiga yajin aikin ne, domin kokawa da yadda ta ce jami'an tsaron Najeriyar na kashe mambobinta ba gaira babu dalili, tare kuma da kwace masu motoci ba bisa ka'ida ba.

Yajin aikin dai ya fara haifar da layuka a gidajen mai a wasu sassan kasar.