China ta ce zata goyi bayan hadewar Koriya ta Kudu da ta Arewa

Kakakin Kasar China

Bayanan sirrin Amurka na baya bayannan da Wikileaks ya fitar sun nuna cewa wasu jami'an gwamnatin kasar China sun furta cewar aminiyarsu Koriya ta arewa ta fara kai su magaryar tukewa.

Wani babban jami'in gwamnatin Koriya ta Kudu ne ya ambato wasu manyan jami'an gwamnatin China suna cewa Beijing a shirye take ta yi marhabin da hadewar kasashen Koriyan biyu muddin dai baza su juya mata baya ba.

China dai ta ki cewa uffan game da bayanan sirrin.

Mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin wajen China Hong Lee, yace China ta ga rahotan tana kuma fatan Amurka zata warware batutuwan da aka tabo a ciki.

Saidai kuma ya kara da cewa Sin ta dade tana kokarin gyara alakar da ke tsakanin Koriyoyin biyu.

Yace tun kimanin shekara da shekaru da suka shude Sin da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin ke ta aiki tukuru wajen ganin an samu zaman lafiya da daidaito a yankin Korea.