Dokar hana 'yan luwadi shiga rundunar sojin Amurka

Sakataren tsaron kasar Amurka, Robert Gates
Image caption Sakataren tsaron kasar Amurka, Robert Gates ya bukaci majalisar dokokin Amurka data dage haramcin da aka sanyawa 'yan luwadi shiga cikin rundunar sojin kasar

Ma'aikatar tsaro ta Amurka ta ce mai yiwuwa a dage haramcin da aka sanya a fili na 'yan luwadi a rundunar sojojin kasar ba tare an yi wata illa ga rundunar sojojin ba.

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates, ya ce akasarin sojojin na goyon bayan daukar wannan mataki, koda yake ya amince cewa wani bangare na sojojin ruwan kasar dake da maza zalla na dari-dari da yin haka.

Mista Gates ya kuma bukaci Majalisar dokokin Amurka data dage haramcin data sanya akan sojoji maza 'yan luwadi da kuma mata dake madugo shiga rundunar sojin kasar, yana mai cewa haka ba zai kawo wani gagarumin sauyi ba kamar yadda wasu ke fargaba.

Sakataren tsaron ya amince cewa a wani bangare na rundunar sojojin dake da maza zalla, akwai wadanda ke matukar dari dari da dage wannan haramcin.