Gwamnan Babban Bakin Najeriya bai janye zarginsa ba

Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Baki bai daidaita ba a majalisar

A Najeriya dazu ne Ministan Kudi da kuma Gwamnan Babban Bankin kasar suka bada bahasi a gaban wasu kwamitocin majalisar dattawan kasar dangane da zargin cewa, majalisun dokokin kasar ne suke lashe kashi 25 cikin dari na kasafin kudin kasar.

'Yan majalisar dai sun husata dangane da wannan furuci da Ministan Kudin ya furta.

Ya ce 'yan majalisar kasar ne ke lashe kashi ashirin da biyar a cikin dari na kasafi kudin kasar.

Cikin 'yan kwanakin nan dai anyi ta sukar 'yan majalisar dokokin Najeriyar dangane da makuden kudaden da ake biyansu.

A zaman na dazu dai an yi ta musayar kalamai tsakanin bangaren majalisar da kuma gwamnan babban bankin Najeriyar.

Malam Sanusi Lamido Sanusi ya tabbatar da yin kalamansa, ya kuma ki janye zargin.