An rataye wata mata a Iran

Shahla Jahed
Image caption Shahla Jahed lokacin shari'arta a shekara ta 2004

Rahotanni daga kasar Iran na nuna cewa, an rataye Shahla Jahed bayanda aka same ta da laifin kashe matar wani sanannen dan kwallon kafar kasar.

Shahla Jahed, mata ce ko kuma masoyiyar Naseer Muhammad Khani, na wani takaitaccen lokaci.

Da a suba ne aka zartar da hukuncin kashe Shahla Jahed. Sai dai ana gab da za a zartar da hukuncin dai an daukaka kara.

Rahotanni sun bayyana cewa iyalan Shahla da kuma ayarin wadansu jami'ai sun shafe fiye da sa'a guda suna rokon iyalan wadanda aka yi wa rashin da su yi mata afuwa.

A karkashin dokar kasar Iran, za'a iya fasa aiwatar da hukuncin kisa idan iyalan wadanda aka yi wa rashin suka hakura. Sai dai iyalan wadanda aka yi wa rashin sun ki amince wa da bukatar.

Kungiyoyi sun soki hukuncin

Da misalin karfe biyar na safe ne dai aka tafi da Shahla wani wurin dake da kwazazzabai a gidan kason Evin da ke birnin Tehran.

Rahotannin daga kafar dillancin labaran Iran ta bayyana cewa Shahla ta yi addu'a a zuci, kafin daga baya ta fashe da kuka.

Sannan dan wadda aka ce ta kashe din ya ture kujerar da kafafunta ke kai. Sai igiya ta rataye wuyan Shahla wadda ke da shekaru arba'in a duniya.

Ita dai Shahla ta kasance matar wucin gadi ga wani shahararren dan wasan kwallon kafa Nasser Mohammaed Khani.

A karkashin dokar Iran, an yarda mutum ya iya aurar mata na wucin gadi, baicin matarsa ta dindindin.

Kungiyoyin kare hakkokin bil adama sun bayyana cewa sam ba'a yi adalci a shari'ar da aka yi wa Shahla Jahed ba.